Friday, 20 April 2018

Hukumar 'Yan Sanda Ta Yi Wa Magu Karin Girma

Hukumar 'yan sanda ta kasa, a yau Juma'a ta sanar da karin girma ga manyan jami'an 'yan sanda 18. Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu na daga cikin wadanda aka karawa girman.

Aminu Saira na murnar zagayowar ranar haihuwarshi


Kalli kek na musamman da aka wa Sani Danja dan tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi


Kalli wani hoton barkwanci da akayi akan maganar Buhari ga matasa


Hoton Hadiza Gabon da mahaifinta

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wannan hoton tare da mahaifinta, ta bayyanashi a matsayin masoyinta na farko, muna fatan Allah yakai Rahama kabarinshi, muna mata fatan Alheri.

Arsene Wenger zai bar Arsenal a bana

Kocin kulob din Arsenal Arsene Wenger zai bar kungiyar a karshen kakar bana, bayan da ya shafe kusan shekara 22 a kulob din. Kocin dan kasar Faransa, zai bar kungiyar ne shekara daya kafin sabuwar kwantiraginsa ta zo karshe.

'A daren da mijinta ya mutu, Maryam Sanda tayi yunkurin caka mai wuka da fasassar kwalba sau 3'>>inji shaida

A cigaba da shari'ar matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, Alkalin kotun ya fara sauraron shaida na farko da ya bayyana abinda ya sani dangane da kisan mijin Maryam din watau Bilyaminu Bello da a gurin tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Halliru Bello.

Masa'uda 'yar Agadas 'yar kwalisa

Jarumar fina-finan Hausa, Masa'uda 'yar Agadas kenan a wadannan hotunan nata da suka dauki hankula.

'Idan kaje Abuja ka bani mukamin me baka shawara'>>Aminu Bono ya gayawa Lawal Ahmad

Tauraron fina-finan Hausa kuma dan takarar majalisar tarayya, Lawal Ahmad tare da me shirya fina-finai, Aminu S. Bono kenan a wannan hoton nasu da suka haskaka, aminun yace wa Lawal idan yaje Abuja yana so ya bashi mukamin me bashi shawara.

Maryam Yahaya 'yar kwalisa

Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar.

Karin hotuna daga shagalin cikar Idris Ajimobi shekaru 30

Dan gidan gwamnan Oyo, Idris Ajimobi Angon Fatima Abdullahi Umar Ganduje ya cika shekaru talatin da haihuwa, an shiya mishi liyafa da shagali na musamman dan tayashi murna, anan karin hotunane inda yake tare da amaryarshi.

Karin hotuna daga gurin liyafar cin abinci da sarauniyar Ingila ta shiryawa shugabannin kasashe da matayensu

A jiyane, sarauniya Ingila, Queen Elizabeth ta shiryawa shuwagabannin kasashe renon kasar Ingilar liyafar cin abincin dare tare da matayensu, shugaba Buhari da uwargida A'isha Buhari sun halarci gurin liyafar, anan karin hotunane daga gurin shagalin.

Kalli kayan tsubbun da aka kama tsagerun da suka saci sandar majalisa da su

A jiyane hukumar 'yan sanda ta kamo mutanen da suka sace sandar ikon majalisar tarayya, a Abuja, wani jami'in 'yansandan ya shaidawa gidan talabijin na TVC cewa an kama tsagerun da sukayi satar sannan kuma an nuna wasu kayan tsubbu da aka kamasu dasu.

'Babu cin hanci a gwamnatin shugaba Buhari'>>Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa irin matakan da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu buhari ta dauka yasa ba'a samu cin hanci karkashin gwamnatin tasu ba.

Kalli yanda turawa suka ki durkusawa dan gaisheda wani basaraken Yarbawa

Wannan hoton yanda aka yiwa wasu turawa jagorane zuwa fadar wani basaraken Yarbawa, Oni of Ife, 'yan Najeriyar da suka musu jagora sun durkusa akan gwiwoyinsu suka gaisheshi amma turawan na zaune akan kujera.

Hotunan kamin biki na Ibrahim Sharukan da Amaryarshi

Jarumin fina-finan Hausa, Ibrahim Sharukan kenan tare da wadda zai aura a wadannan hotunan nasu na kamin biki, muna musu fatan Alheri da fatan Allah basu zaman lafiya.

Sani Musa Danja na murnar zagayowar ranar haihuwarshi

Tauraron fina-finan Hausa da turanci, Sani Musa Danja, Zaki, na murnar zagayowar ranar haihuwarshi, muna tayashi murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

Rahama Hassan ta haifi diya mace

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Hassan ta haifi diya mace, muna tayata da megidanta murna da fatan Allah ya rayata rayuwa me Albarka.

'An yiwa kalaman shugaba Buhari mummunar fahimta: Cikin Raha ya furtasu'

A Najeriya, wasu mukarraban shugaban kasar sun ce an yi mummunar fahimta game da kalaman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa mafi yawan matasan kasar cima zaune ne.

Thursday, 19 April 2018

Shugaba Buhari da uwargida A'isha akan hanyarsu ta halartar liyafar da sarauniyar ingila ta shirya musu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari tare da uwargida Hajiya A'isha Buhari a lokacin da suke kan hanyar halartar liyafar cin abinci dare da sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta shiryawa shuwagabannin kasashe renon ingila da matansu acan Ingilar.