Pages

Saturday 15 October 2016

An gayyaci Rahama Sadau Masana'antar fina-finan kasar Amurka

Shahararren mawakin kasar Amurkan nan wanda akafi sani da Akon wanda a yanzu ya shiga harkan yin fim da kuma wani shima dan fim din kasar Amurka wanda ake kira da  suna Jeta Amata dukansu bakar fatane saun gayyaci Rahama Sadau zuwa can Amurka masana antar fina finan da akekira da Hollywood inda suke shirin wani fim da zai kawosu kasashen Afrika irin su Africa ta Kudu da Senegal da nan Najeriya.


Amma abinda bai fito fili ba dangane da wannan labari shine ko sunaso su saka ta cikin fim din da suke shiryawane kokuwa? To amma hausawa na cewa idan kaga kare na shin shina takalmi to daukarshi zaiyi.

Idandai har saka Rahama Sadau zasuyi cikin fim din nasu to akwai tambayoyi da mutane da dama zasuso suji amsoshinsu kamar haka.

Masana antar fim ta kasar Amurka watau Hollywood gurine wanda akemai kallon da cewa na fitsararrun mutane wadanda basuda kunya kuma wannan haka yake koda a gurin wasu yan kasar ta Amurka.

Wannan zai kawomu ga maganar rungume-rungume da sumbata da rike hannu kai harma da zinace zinace da ake nunowa a fina finan kasar Amurka.

To idan Rahama Sadau zatayi fim a irin wannan masana'anta tsakanin mutane da basu dauki bayyana tsiraici komaiba kuma a matsayinta na musulma. Zata bukaci cewa bazatayi irin wadancan abubuwa da muka lissafa a bayaba?

Sannan idan tace bazatayiba su masu shirin fimdin zasu amince da hakan kuwa? Musamman idan labarin fimdin da akeyi yazo da bukatar hakan?

To harya zuwa yanzudai Rahama Sadau bata bayyana cewa ko zata amsa goron gayyatar da akayi mata zuwa masana'antar fim ta kasar amurkan ba. Saidai ta bayyana jin dadinta da gayyatar da aka mata.

A yanzu haka Rahama Sadau tana kanyin wasu fina finan turanci guda biyu.

Kwanakin bayane dai aka kori Rahamar daga masana'antar fina finan hausa bayan tayi wata waka da wani mawaki classiq wanda aka ganta tana rungumarshi.

Hotunan yan fimdin kasar Amurka da suka gayyaci Rahama Sadau

Hoton Akon

Hoton Jeta Amata

No comments:

Post a Comment