Pages

Sunday 19 March 2017

Saurayin Maryam Booth ya yaudareta

A wani sako data fitar a shafinta na sada zumunta da muhawara, jarumar fim din hausa, Maryam Booth(Dijan Gala), ta bayyana yanda wani saurayinta ya yaudareta, amma bata fadi sunanshiba, tace ta bashi duk(soyayyarta)(..?..) ta kuma yarda dashi, duk da cewa mutane sunata gayamata cewa tayi hankali dashi karta saki jiki dashi, amma shaukin so yasa bataji abinda mutane ke gayamata ba, ta kara da cewa bata taba cin amanarshi ba da wani tsohon saurayinta ba(...kome take nufi da hakan?...) haka kuma yasha gayamata maganganun karya dangane da tsofaffin 'yan matanshi, tace amma duk da haka sai gashi a karshe ya yaudareta, ya tafi ya barta, tace Allah ne kadai yasan irin halin data shiga ciki kuma shine zai kawo mata dauki.

A karshe tace yanzu(ta tsani maza) bata bukatar ganin wani namiji a rayuwarta.



Allah sarki gaskiya wasu mazan basu kyautawa sai mace ta amince dakai, wanin ma sai yayi amfani dason da take mishi suyi abinda bazai iya faduwaba a bainar jama'a, kuma ita saboda so ko kuma tana tsoron rabuwa dashi da kuma ganin kamar da gaske yake aurenta zaiyi sai ta yarda dashi amma a karshe sai ya watsar da ita. Mata ayi hattara, duk da yake kuma kunada naku matsaar....

Zan iya tunawa a ranar da Maryam Booth take murnar zagayowar ranar haihuwarta, ta fitar da wani sako inda take cewa tana kyautata zato da tsammanin cewa ranar haihuwarta me zuwa a gidan mijinta zatayita(wato tayi aure kamin lokacin) kuma ga dukkan alama da wannan saurayin nata ne da tace ya yaudareta take tsammanin zasuyi aure, amma gashi yanda abin ya kasance.

Haka kuma a 'yan kwanakinnan Maryam ta rika saka wasu sakwannin dake nuna alamar cewa tana cikin wani halin damuwa na soyayya, inda ta rika rubuta sakonni kamar, koma meme ya faru, rayuwa zataci gaba da gudana, da kuma ta yaya zaka rika bada hakuri akan laifin da kayi bayan ayyukanka na zahiri basu nuna cewa kayi nadamaba?

Haka kuma a baya bayannan Maryam ta fitar da wani sako inda take cewa itafa duk Duniyarnan kaninta Amude Booth ne ta yarda dashi, duk irin wadannan kalamai dama an saba jinsune daga bakin wanda ya shiga rudanin soyayya.

Munawa Maryam fatan Allah yasa su shirya da wannan saurayi nata ko kuma idan abin nasu bana shiryawa bane to Allah ya hadata da wanda ya fishi, da kuma zai sota da gaskiya. Amin.

No comments:

Post a Comment