Pages

Wednesday 15 November 2017

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya kunyata gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose akan maganar gyaran ilimin jihar Kaduna

Gwamnan Jihar Ekiti, Peter Ayodele  Fayose yayi wani rubutu a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter inda ya gargadi mutanen Najeriya cewa abinda jam'iyyar APC ta saka a gaba shine korar ma'aikata, an kori malaman makaranta daga aiki a jihar kaduna kuma shugaban kasa Buhari ya nuna goyon baya.



Koda gwamnan jihar kaduna Malam Nasiru El-Rufai yaga wannan batu sai ya mayar wa da Fayose martanin cewa, "bawai muna koran ma'aikata daga aiki bane a jihar kaduna ba, muna maye gurbin mutanen da bai kamata a kirasu malamai bane da wadanda suka cancanta dan mu tanadarwa 'ya'yanmu da jikokin mu masu zuwa nan gaba tsarin ilimi me kyau".

Tun bayan da gwamna El-Rufai ya mayarwa da Fayose martanin wannan maganar, abin ya dauki hankulan mutane sosai, an yita nanata maganar ta El-Rufain da kuma danna alamar cewa maganar ta dace. Zuwa yanzu dai Fayose bai sake yin magana akan batun ba.
Shidai Fayose ya fara nuna burinshi na son tsayawa neman takarar shugabancin kasarnan akarkashin jam'iyyar PDP.

No comments:

Post a Comment