Thursday, 15 February 2018

Real Madrid ta lallasa PSG da ci 3-1

Real Madrid ta ci Paris St Germain 3-1 a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai da suka kara a ranar Laraba a Santiago Bernabeu. PSG ce ta fara cin kwallo ta hannun Adrien Rabiot a minti na 33 da fara tamaula, kuma daf da za a tafi hutu Madrid ta farke ta hannun Cristiano Ronaldo a bugun fenariti.


Saura minti bakwai a tashi daga wasan Cristiano Ronaldo ya ci na biyu, sanan Marcelo Vieira Da Silva ya kara na uku a raga.

Real da PSG sun kara a gasar cin kofin Zakarun Turai a kakar 2015/16, inda suka tashi canjaras a Faransa a wasan farko a ranar 21 ga watan Oktoba, a wasa na biyu a ranar 3 ga watan Nuwamba Real ta ci 1-0 a Spaniya.

PSG zata karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris din 2018.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment