Dan wasan Manchester United, Zlatan Ibrahimovic na shirin barin kungiyar tun kafin yarjejeniyarsa ta kare a Old Trafford. Babu wata sanarwa daga United, amma an ce Jose Mourinho ya amince Ibrahimovich ya bar kungiyar tun kafin kwantiragin da ya saka hannu da za ta kare a ranar 30 ga watan Yuni ta cika.
Har yanzu ba a fayyace inda Ibrahimovich zai koma da murza-leda ba, amma ana rade-radin cewar zai koma buga gasar Amurka a kungiyar LA Galaxy.
Ibrahimovich mai shekara 36, ya koma United daga Paris St-German a shekarar 2016.
Tshohon dan wasan tawagar kwallon kafar Sweden ya ci kwallo 29 a karawa 53 da ya yi wa United, amma har yanzu bai warke daga raunin da ya ji a wasa da Anderlecht a watan Afirilu ba.
bbchausa.
No comments:
Post a Comment