fbpx
Sunday, April 18
Shadow

2023: Zan tsaya takarar Shugaban kasa, in kawo karshen matsalar tsaro cikin shekaru biyu>>Okupe

Wani mai magana da yawun tsoffin shugabannin kasa biyu (Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan), Dokta Doyin Okupe, a cikin wannan rubutun, ya ce zai tsaya takarar Shugaban kasa a 2023 idan har matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta bata kare ba.

Yace; zan tsaya takarar Shugaban kasa a 2023 idan har yan bindinga, masu satar mutane, Boko Haram da sauran masu aikata laifuka suka ci gaba da addabar kasar nan.

Ya kara da cewa bai kamata a bar abubuwan suyi ta tafiya a haka ba, ya shi mutum ne da ya kasance makusancin jajirtattun tsofaffin Shuwagabannin kasa 2 (Olusegun Obasanjo da Goodluck Ebele Jonathan) don haka yana gogewa da kuma kwarewa a harakar mulkin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *