Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a wannan sallar Layya da aka yi yayi ta a fadarshi ta Villa dake banban Birnin tarayya, Abuja saboda zuwan cutar Coronavirus/COVID-19.
A baya shugaba Buhari tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2015 a Daura yake yin Sallah inda jama’a ke masa Rakiya zuwa Masallaci sannan su mai rakiya zuwa gida idan ya kammala sallah.
Da yake jawabi a lokacin Sallar bana, Sarkin Daura, Me martaba, Umar Farouk ya bayyana cewa sun yi kewar dan nasu.