fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Abu daya ne ya ke hanamu kai Sojoji mu murkushe ‘yan Bindiga>>Shugaba Buhari yayi Allah wadai da sace daliban Jangebe

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da sace dalibai Mata a Jangebe ta jihar Zamfara.

 

A sanarwar da ya fitar shugaban yace babu wani me laifi da ya fi karfin Gwamnati.

 

Yace dalili daya dake hana Gwamnatin daukar mataki akan ‘yan Bindigar shine saboda kada a kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba. Yace za’a iya kai Tarin Sojoji kauyukan da ake wannan sace-sace amma abu daya ne ke takawa Gwamnati Birki shine kada a kashe wanda akale tsare dasu da kuma wanda basu ji ba basu gani ba.

 

Yace maganar garkuwa da mutane abu ne me matukar Hadari wanda yana Bukatar a bishi a sannu sannan a yi hakuri dan a samu a kubutar da wanda aka sace ba tare da an ji musu rauni ko mummunan kisa ba.

 

Yace ‘yan Bindigar kada su taba Tunanin cewa sun fi karfin Gwamnati ko kuma daga musu kafar da ake tsoro ne ko gajiyawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *