Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa aiki yawa jami’an tsaron Najeriya yawa inda a yanu suna aiki a kusan jihohi 34 na kasarnan.
Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a ganawarsa da Channelstv. Yace yanzu haka jami’an tsaron na ‘yansanda da sojoji na daukar karin ma’aikata inda ake basu horo.
Da yake magana akan rikicin Fulani Makiyaya da Manoma, kakakin Shugaban kasar ya bayyana cewa, shugaba Buhari ba mutum ne me son yawan fariya ba, yace akwai Fulani da yanzu haka ana Tuhumar su da laifuka daban-daban musamman a jihar Benue.