fbpx
Sunday, March 7
Shadow

An bayyana Mata a matsayin wanda ke da kaso mafi yawa da aka tabbatar dake Dauke da Cuta mai sarke Numfashi a jihar Kwara

An bayyana Mata a matsayin wanda ke da kaso mafi yawa da aka tabbatar dake Dauke da Cuta mai sarke Numfashi a jihar Kwara
A wata sanarwa da kwararriya mai bincike kan yaduwar cututtuka da shawo kan cutar a jihar Kwara Dakta Khadija Kamaludeen ta fitar ta bayyana cewa Jihar ta gwada mutane 17,581.
Mai binciken ta bayyana hakan ne a wani taron yaki da cutar Korona na kullum dake gudana a jihar inda ta bayyana cewa Mata a jihar Nada kaso mafi yawa na masu Dauke da cutar inda mata keda kaso 56.6 yayin da maza keda kaso 46.4.
A cewarta, Wadanda aka tantance mafiya yawan su ‘yan shekaru 25 zuwa 29 ne.
Ta kuma kara da cewa , A yanzu jihar nada Dakunan gwaje-gwaje har guda 12 a kananan hukumomi 16 dake jihar.
Da take bayyana mutane da cutar ta kashe a jihar ta ce a kalla mutane 45 ne aka bayyana mutuwarsu a sanadin cutar a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *