fbpx
Sunday, April 18
Shadow

An gano cewa matarnan da ta yi lalata da Yaro dan shekaru 13 ta yi amfani da maganin saka Bacci

Matarnan Precious Teya data yi lalata da karamin yaro dan shekaru 13 a kasar Zimbabwe wadda ta bayyana a gaban Kotu ranar 26 ga watan Fabrairu,  wasu karin bayanai sun bayyana kan yanda lamarin ya faru.

 

Yaron ya hadu da matar me shekaru 26 ne ta shafin masoya na yanar gizo inda suka amince su hadu su yi lalata. Ya amince zai biyata Dala 20, sannan kuma zata je gidansu inda zasu yi amfani da maganin bacci su baiwa ‘yan uwamsa dan kada su ga abinda ke faruwa.

 

Saidai daga baya yaron ya tsorata inda yace ya fasa, amma matar tace sai sun yi. Taje gidansu kuma sun baiwa ‘yan uwan yaron maganin bacci Sannan suka yi lalatar. Saidai bayan da suka gama, tace ba zata karbi Dala 20 ba sai dala 120, yaron yace mata bashi dasu bashi da dalilinsu. Saidai ta takura masa akan hakan.

 

Yaron ya je gidan makwabcinsu inda ya nemi ya ranta masa kudi, koda makwabcin ya tsaurara bincike akan abinda yaron zai yi da kudin, Dai ya gano abinda ya faru inda a nan ne ya gayawa mahaifansa aka kama matar.

 

Hutudole ya kawo muku Rahoton yanda lamarin ya faru a baya inda matar tace, Yaron ne yace mata yanaso dan haka bata aikata laifin komai ba.

 

Rahoton namu ya watsu sosai tsakanin Ma’abota shafukan sada zumunta inda akai ta muhawara akai, da dama sun yi Liking wasu sun yi Sharing hakanan shafuka da yawa na Hausa Sun kwafi labarin daga shafinmu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *