fbpx
Thursday, April 22
Shadow

An kama mutane shida da ake zargi da yin garkuwa da mutane a Abuja

Rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya, Abuja da ke aiki a kan sahihan bayanan sirri ta kama mutane shida da ake zargin masu satar mutane ne a kan hanyar Apo.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, ASP Yusuf Mariam ta fitar, ta bayar da sunayen wadanda ake zargin kamar su Frank Ozor 26yrs, Nweke Uche 19yrs, Chester Uzor 25yrs, Chukwu Bethrand 27 yrs, Chukwu Samuel 25yrs da Kelechi Ngene 26 yrs.

ASP Mariam ta kara da cewa kamu da akayi wadanda ake zargin yasa sukai nasarar kubutar da wasu mutune 2 da akayi garkuwa da su.

Bugu da kari, rundunar tana aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro, manyan masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma don kawar da masu aikata laifuka daga babban birnin tarayya, Abuja.

ASP ta kuma yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankulansu kuma su kasance masu bin doka da oda, sannan su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba a ofishin ‘yan sanda da ke kusa da su ko kuma su tuntumbe su ta hanyar wadannan lambabobin yan: 08032003913, 08061581938, 07057337653 da kuma 08028940883.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *