fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

An kama wani Lauya mai shekaru 56 bisa zargin yiwa yarinya ‘yar shekaru 14 fyade har tayi ciki a Jihar Oyo

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Oyo ta cafke wani mutum mai shekaru 56, Remi Oladiti, wanda ke ikirarin shi lauya ne, bisa zargin bai wa yarinya yar shekara 14 kwaya tare da yi mata fyaden da yayi sanadiyyar ta dauki ciki a unguwar Bodija da ke Ibadan.

Kwamishanan ‘yan sanda na jihar, Misis Ngozi Onadeko, wacce ta bayyana hakan yayin da take zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, ta ce an tura yarinyar ne aike a lokacin da Oladiti ya same ta kuma ya ba ta wani abin sha mai wanda aka zubawa Kwayoyi a ciki.

Yarinyar an ce ta sume bayan ta sha abin, sai kwatsam ta farka ta tsinci kanta tsirara a kan gadon mutumin.

Shugaban ‘yan sandan ya ce binciken likita ya tabbatar da cewa yarinyar na dauke da juna biyu na makonni 29.

Wanda ake zargin yace lalle yasan da yarinya kuma sunyi tarayya da juna amma be bata wani abu mai gusar da hankali ba.

Yayin da yake magana da manema labarai, Oladiti ya yi ikirarin cewa bai tilasta wa yarinya ba a lokacin da ya kusan ce ta, inda ya kara da cewa ta fada masa cewa shekarunta 18 ne.

A halin yanzu yana hannun yan sanda domin cigaba da gudanar da bincike kafin a tura su a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *