Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar Sokoto sun kama wani dan shekaru 36 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Nkem Timothy, mai suna Auwalu Audu, yayin da yake kokarin tsallakawa zuwa Algeria ta Jamhuriyar Nijar da wasu 62 rufe da ake zargi zama hodar iblis ce.
Daraktan hulda da jama’a na Hedikwatar NDLEA, a Abuja, Mista Femi Babafemi, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 28 ga watan Fabrairu, ya ce sinadarin wanda ya kai nauyin 1.550kg, ya kiyasta darajar kusan Naira biliyan daya.
Ya kuma ce an boye wasu haramtattun magunguna a cikin kwalaben yoghurt.
Ya kara da cewa, a halin yanzu jami’an nasu sun fara bincike don gano wanda ya dauki nauyinsa da sauran mambobin kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi.
Babafemi a cikin sanarwar ya ce wanda ake zargin yana zaune a Algeria, an kama shi a kan babur a kusa da yankin kaya a iyakar Illela yayin da yake kokarin tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar.