fbpx
Sunday, March 7
Shadow

An kama wani mutum mai shekaru 53 da laifin dabawa makwabcinsa kwalba har lahira a Legas

Jami’an ‘yan sanda da ke aiki a Makinde Division a jihar Legas a ranar Litinin, 22 ga watan Fabrairu sun kama wani mutum dan shekaru 53, mai suna Sunday Amaefula da ke layin No 8 Akpaku, Mafoluku, Oshodi, jihar Legas bisa zargin daba wa makwabcinsa mai Suna Chibuike Nwanne, kwalba har lahira.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ademuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce binciken da’ yan sanda ya gudanar ya nuna cewa mamacin ya samu sabani da dan uwan ​​wanda ake zargin mai suna Ifeanyi Emmanuel, kafin wanda ake zargin (Sunday Amaefula) ya daba wa marigayin kwalba a cikin gidansu.

Adejobi ya kara da cewa marigayin, wanda ya yi aure a shekarar da ta gabata, ya bar matar da ke da ciki.

Ya kara da cewa har yanzu suna kan bincike kafin a tura fayil din zuwa kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *