fbpx
Saturday, March 6
Shadow

An Kama Wasu Da Suka Bayyana Kansu a Matsayin Jami’an Soja Da Miyagun Kwayoyi Manyan Dauri Masu Nauyin Kilogram 234 a Jihar Kwara

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin sojojin bogi ne a cikin wani sabon Toyota Hilux Jeep dauke da muggan kwayoyi 394 wadanda aka boye a sassa daban daban na motar.
Kakakin hukumar, Jonah Achema, ya fada a ranar Talata a Abuja cewa wadanda ake zargin hafsoshin sojan na jabu ne; Mohammed Nura da Abubakar Dahiru, sun shiga hannun jami’an hukumar ta NDLEA ta jihar Kogi a kan babbar hanyar Okene-Lokoja a ranar Litinin, 15 ga Fabrairu, 2021.
Ya ruwaito kwamandan, hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi ta jihar Kogi, Mista Adewunmi Alfred, yana cewa an binciki samfurin VIP na Hilux Jeep yadda ya kamata yayin da aka gano manyan dauri 394 na wiwi a bangarori daban-daban na motar.
“Bincikenmu na farko ya nuna cewa an dauke kayan ne daga Lagos aka nufa kaisu jihar Kano,”, Alfred ya bayyana daga cikin wani taƙaitaccen bayani daga Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) a ranar Litinin.
“Duk da cewa mutanen biyu sun bayyana kansu a matsayin jami’an soji amma hakan bai sa mutanenmu gaza yin bincike sosai ba game da motarsu kuma sakamakon haka shi ne gano muggan kwayoyi da aka sanya a cikin kowane bangare na motar. Lallai, muna zargin mutanen biyu da cewa jami’an sojan bogi ne har sai an tabbatar da sabanin haka. ”
Ya kara da cewa an kwace motar, an kame muggan kwayoyi tare da tsare wadanda ake zargin don ci gaba da bincike.
Ya kara da cewa, “bincike ya fara kuma za a tura sakamakon don ci gaba da bayar da umarni da kuma daukar matakin da ya dace.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *