fbpx
Sunday, April 18
Shadow

An kama wasu mutane biyu da ake zargin dillalan miyagun kwayoyi ne a jihar Kuros Riba

Wasu mutane 2 da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi (Effangha Effangha mai shekaru 37, da Eno-Obong Udome mai shekaru 34), sun shiga hannun jami’an tsaro soja na “Operation Akpakwu” a Jihar Kuros Riba.

An kama wadanda ake zargin a ranar Alhamis da Juma’a 25, 26 ga Fabrairu, a kan titin Nelson Mandela a Calabar da Ekpenyong Ekpo a karamar hukumar Akpabuyo ta jihar.

Rundunar Sojojin ta 13 Brigade dake Calabar ta mika mutanen biyu da ake zargi dillalan miyagun kwayoyi ne ga hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) don ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *