Yansanda a jihar Legas sun bayyana cewa, sun kama wasu abokan aikinsu 4 da suka karbi Dubu 70 daga hannun dalibi dan shekaru 16 a NJBA Junction dake Isheri na jihar.
Kakakin ‘yansandan Jihar Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Juma’a. Yace an dauki matakin kama ‘Yansandan masu mukamin insfekta ne bayan da bidiyon abinda suka yi ya watsu a shafukan sada zumunta.
Yace an mayarwa da matashin dalibin kudinsa sannan kuma kwamishinan ‘yansandan yace a yi abinci ke dan hukunta su idan an samesu da laifi dan ya sama darasi ga ‘yan baya.