Akalla mutane 35 aka ba da rahoton an kashe bayan wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari a kauyen Sabuwar Tunga, gundumar Dankurmi da ke cikin Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara a daren Alhamis, 25 ga Fabrairu.
Yan bindigar sun afkawa mutanen ne a kan babura tare da muggan makamai suka razana mazauna kauyen.
Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun shirya shi sosai kafin su afkawa garin.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar bayan sun far wa kauyen sun kwashe dabbobin suka gudu zuwa daji.