A jiyane dai aka rika yada jita-jita cewa Fulani makiyaya sun kutsa cikin gidan Farfesa Wole Soyinka. Saidai daga baya an musanta wanan zargi.
Amma kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC ta bayyana cewa bafa Fulanine suka shiga gidan na Soyinka ba, Wani Bayerabene.
A sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin shugaban ta, Farfesa Ishaq Akintola ta bayyana cewa, an zargi Fulani daga Arewa da shiga gidan Soyinka amma maganar Gaskiya itace ba Fulani bane, Bayerabene me suna Kazeem Sorinola.