fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Ana ci gaba da mace-mace a Kano duk da karyata hakan da gwamnatin jihar ta yi

Mace-mace da ba’a saba ganin irinsu ba a jihar Kano na ci gaba da aukuwa duk da karyata hakan da mahukuntan jihar ke ci gaba da yi.

 

A makon daya gabatane Daily Trust ta  ruwaito cewa an samu mace-mace kusan 150 a cikin kwanaki 3, abinda gwamnatin jihar ta musanta.

 

Saidai a ci gaba da binciken jaridar wasu mazauna birnin sun bayyana yanda mace-macen ke ci gaba da aukuwa.

 

A zangon Barebari kawai, Jaridar ta samu Rahoton cewa mutane 15 ne suka rasu tsakanin Laraba zuwa Juma’a.

 

A makabarkar Dandolo, tsakanin Laraba zuwa Juma’a, An samu Rahoton cewa an binne gawarwaki 67.

 

Rahoton yace Asibitin Aminu Kano wanda shine babban asibiti a cikin Garin Kano an kulleshi inda aka ware wani waje da ake duba marasa lafiya dake zuwa daga gida da basu da yawa.

 

Mustapha Muhammad Zakari, wani mazaunin Gwammaja ya shaida cewa akwai mahaifiyarsa dake fama da ciwon suga, ciwon nata ya tashi suka kaita Asibitin Dala amma aka ki karbarta, yace suna kan hanyar neman Wani Asibitin ta rasu.

 

Shima wani Aminu Ibrahim ya bayyana cewa, Mahaifinsa ya kwanta Rashin Lafiya kuma ya kaishi Asibitin Nasarawa amma aka ki karbarsa Saboda wai Babu Likita.

 

Yace sun kaishi Wani Asibitin ‘yan Kaba inda aka ce Zazzabin Malaria da Taipof ne ke damunshi. Yace bayannan sai ya rasu.

 

Ana ta’allaka yawan mace-mace da rufe Asibitoci saboda dokar hana zirga-zirga da ka saka a Kanon wanda hakan yasa marasa Lafiya da dama basa samun kulawa.

 

Tuni dai Rahotanni suka bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara binike kan musabbabin wannan mace-mace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *