fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Arsenal ta lashe kofin FA Cup bayan sun ba Chelsea kashi 2-1, yayin da Aubameyang yaci gabadaya kwallayen

A yau ranar sati daya ga watan augusta aka buga wasan final na gasar FA Cup tsakanin Arsenal da Chelsea, kuma tawagar Mikel Arteta tayi nasarar ba Chelsea kashi har 2-1.

Pierre Emerick Aubameyang ne yayi nasarar ciwa Arsenal gabadaya kwallayen guda biyu, yayin da yaci kwallo guda kafin aje hutun rabin lokaci kuma ya kara wata bayan an dawo daga hutun. Shima Christian Pulsic yayi nasarar ciwa Chelsea kwallo guda amma sai dai ya bar wasan saboda rauni.
Pulsic yasa tawagar Lampard sun fara jagorantar wasan cikin minti biyar, amma Aubameyang ya ramawa Arsenal kwallon kuma ya kara wata a minti na 67. Kovakic ya samu yalon kati na biyu bayan ya bugi Granit Zhaka wanda hakan yasa aka ba shi jan kati kuma Chelsea suka gama wasan da yan wasa goma.
Sakamakon wasan na nufin cewa yanzu Arsenal sun gama wannan kakar da kofi kuma sun samu cancanta a gasar Europa League, yayin da Kuma suka rama abinda Chelsea ta yi masu a wasan final na gasar Europa League a kakar wasan bara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *