Ministan yada labarai da Al’adu, Lai Muhammad ya bayyana cewa ba’a Najeriya kadai ake samun matsalar satar dalibai ba, Hadda kasashen Duniya da dama da suka ci gaba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channelstv inda yace ‘yan Bindigar sun fi son su yi garkuwa da mutanen dake da rauni.
Yace a kasar Amurka an samu satar dalibai har kusan sau 4 a shekarar 2020.