fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Ba zan nemi gafara a kan maganar da nayi game da makiyaya ba – Gwamnan Jihar Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce ba zai nemi gafara game da kalaman da ya yi kan makiyaya a makon da ya gabata, yana mai cewa adawa ce kiran sunan kabilar Fulani a matsayin masu kisa da masu satar mutane.

Idan zaku iya tunawa, Gwamna Bala Mohammed, ya sha suka sosai kan furucin da ya yi na cewa makiyaya na dauke da AK-47 don su kare kansu.

Bala Mohammed wanda ya yi magana a ranar Laraba a lokacin da yake kaddamar da allurar rigakafin dabbobi ta shekara 2020/2021, wanda aka gudanar a Galambi Cattle ranch da ke Bauchi, ya ce bai kamata a dangata wata kabila da ta’addanci ba, saboda yin haka na iya haifar da rashin hadin kai a kasar.

Gwamna Bala ha kara da cewa babu wani aibi a cikin maganar da yayi, don haka ba zai nemi gafara a a wajen kowa ba.

A karshe yace Gwamnatinsa za ta tallafawa makiyaya domin rage ta’addanci da kuma kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a Jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *