fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Babu afuwa ga yan bindinga da masu tayar da kayar baya – Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za tayi wa yan bindinga ko masu tayar da kayar baya afuwa ba, yana mai cewa Gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin kawo karshen yan bindinga da sauran masu aikata laifuka.

Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin bude taron hadin gwiwar tsaro na kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Majalisar Sarakunan Gargajiyar Arewa da wakilai daga Gwamnatin Tarayya, ya ce lokaci ya yi da za a dauki masu laifi a matsayin masu laifi kuma a daina danganta ta’addanci da kabilanci.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce, kalubalen tsaro da ke addabar al’ummar kasar, ya yi sanadiyyar sanya ‘yan Najeriya cikin talaucin da kariyar tattalin arziki, don haka ya riga ya umarci shugaban na tsaro da ya samar da tsare-tsare don kawo karshen ta’addanci a ƙasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *