Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19 ba dole bane sai mutum naso.
Karamin Ministan Lafiya, Olurunnimbe Mamora ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi a Arise TV.
A jiyanw dai aka kawowa Najeriya tallafin rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19 din Miliyan 3.9. Mamora yace babu wanda za’a tursasawa yayi.