fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Ban Sa A Kama Hamisu Breaker Ba>>Adam Fasaha

Fitaccen mawakin nan, Adam Fasaha ya musanta jita-jitar da ake ta yadawa cewa ya kama abokin sana’arsa mawaki Hamisu Breaker bisa zargin sa sa yaudaro tsohuwar matarsa, Momi Gombe zuwa cikin masana’antar fim.

 

 

Idan ba a manta ba, tun bayan da Adam Fasaha ya zargi Hamisu Breaker din ne aka soma yada wasu hotuna da aka nuna jami’an tsaro sun kama mawaki Breaker, wanda kuma hotunan an yi su ne da sunan wasa a yayin wani wasa da Breaker ya gudanar a cibiyar wasanni ta Abacha Youth Center dake Kano a shekarun baya.

 

 

A yayin da yake jawabi ta bakin Adam Fasaha, mawaki Aliliyo Mai Waka ya bayyana cewa wasu daga cikin yaran Hamisu Breaker din ne suke ta yada hotunan domin su jawowa Adam Fasaha zagi.

 

 

“Ni Aliliyo Mai waka ina da tabbacin wannan hoton da suke yawo da shi suna cewa wai mun kama Hamisu Breaker ba mu da masaniya akan hakan, suna yin haka ne domin su ga sun wanke kansu daga wancan zargin da ake yi Breaker din. Ko da ba mu kama Hamisu ba kamun da Allah kawai zai yi masa shine babban kamu amma Adam Fasaha ba shi da hannu kan hakan.

 

 

“Sannan Hamisu ya bani mamaki da wai yake cewa wai mun yi masa kage. Ya manta ka taba tura min sako (message) ka ce mun ko yanzu Adam Fasaha idan yana son Momy kai kadai za ka sa ta koma gidansa. Ka manta ka ce mun kai ka bawa Momy Gombe damar auran Adam Fasaha kuma ka ce mun ni ban isa na yi komai a kai ba.

 

 

“Haka kuma ka ce yadda Momy take jin maganarka ko ta mahaifanta ba ta ji kuma kace kai ne ka bata kwarin gwiwar aure.

 

 

“Amma zan yi maka tambaya, mai ya sa lokacin da Momy ta fito daga gidan Adam Fasaha har kawo yanzu baka taba kiran sa ba ka ce mai ya faru tsakaninsa da Momy. A matsayin ka na wanda ya san ta yi aure mai ya sa ka dauke ta a satin kuka tafi shutin din fim. Ina tambayar ka wannan ma kage ne?

 

 

Sannan akwai wata jaruma daga cikin kawayen Momy Gombe amma ta ce a sakaye sunanta ta ce tabbas Hamisu Breaka da Momy sun ci amanar Adam Fasaha kuma Allah kadai zai yi saka masa.

 

 

Daga karshe Adam Fasaha ya godewa Ali Nuhu kan yadda ya yi ruwa da tsaki kan rikicin don ganin ya daidaita lamarin. Ba kamar sauran abokan sana’ar su ba da suka dinga rura wutar rikicin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *