fbpx
Monday, June 14
Shadow

Bayern Munich sun yi nasara a wasan da suka buga da Bayer Leverkusen a yau yayin da suka tashi 4-2

Bayern Munich sun kara matsawa kusa da lashe kofin gasar Bundlesliga karo na 8 a jere yayin da suka yi nasarar jefa kwallaye har guda hudu a wasan da suka buga tsakanin su da Bayer Leverkusen a yau ranar sati 6 ga watan yuni.

Leverkusen sun firgita Munich daga farko yayin da Lucas Alario ya jefa kwallo cikin minti goma na farko a wasan kafin su ci kwallayen su guda hudu, sun ci kwallaye uku kafin a aje hutun rabin lokaci yayin da dan wasan Leverkusen mai shekaru 17 Wirtz yace kwallo ta karshe a wasan.
Kingsley Coman, Leon Goretzaka, Serge Gnabry da Robert Lewandowski sune suka ci kwallayen kungiyar Munich yayain da Lucas Alario da Florian Wirtz suka jefa kwallayen Leverkusen. Yanzu Munich sun wuce Dortmund da maki goma.
Yan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich sun yi kokari sosai wanda har yasa suka yi nasarar jefa kwallaye har guda hudu, Amma sai dai yan wasa su na baya basu yi kokari sosai ba yayin daya kamata ace sun cire kwallaye guda biyu da Leverkusen suka ci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *