Atletico Bilbao ta dake Barcelona da ci 3-2 inda ta dauki kofin Spanish Super Cup.
Wasan ya dauki hankula sosai inda a karin farko a tarihin wasan da ya bugawa Barcelona, Lionel Messi ya samu jan kati saboda dukan dan wasan Bilbao.
Sai da alkalin wasa ya duba VAR sannan ya nunawa Messi jan kati, wanda kuma shine karin farko a wasanni 753 da ya bugawa Barcelona.
Lionel Messi Red Card pic.twitter.com/HjC23gszvR
— MESSI IS THE BEST (@bestismessi) January 17, 2021
Antoine Griezmann ne ya ciwa Barca kwallaye 2 amma Bilbao ta ramasu duka kuma a haka aka tashi wasan. Bilbao ce ta doke Real Madrid kamin zuwa wasan karshe na Spanish Super Cup din.