fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Bidiyo: Yanda Boko Haram sun kai sojojin Najeriya harin kwantan Bauna, Kafar soja ta cire, motarsu na ci da wuta, suna kuka suna caccakar Buratai

Sojojin Najeriya kenan dake yaki da Kungiyar Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas a yayin da kungiyar ta kai musu wani harin kwantan Bauna.

 

A wasu hotunan za’a iya ganin yanda wasu sojojin ke kwakkwance Maganshiyan suna gurnanin Azaba saboda ciwukan dake jikinsu.

 

Wani daga cikin sojojin harin da aka kai ya cire mana kafa, ana kokarin tafiya dashi Asibiti.

A wani Bidiyon kuma wanda shima Boko Haram din suka kaiwa Sojojin Najeriya harin kwantan Bauna, an ga sojojin na kuka suna cewa hukumar Soji ta sayar dasu.

 

Sojan dake daukar Bidiyon yana caccakar shugaban Sojin Najeriya, Janar Buratai inda yake cewa ba zai gana lafiya ba.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa, a ‘yan Kwanakinnan, Sojojin Najeriya da dama ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren na Boko Haram.

Wadanna hotunan wasu Sojojinne da suka ransa rayukansu kuma ake kokarin kaisu makwancinsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *