fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Budurwa ta damfari Saurayin da zai aureta Miliyan 10 inda ta koma soyayya da wani

Wani dan Najeriya,  Ogunshakin Emmanuel dake zaune a kasar waje ya shiga hannun Budurwa mayaudariya.

 

Ya aikewa Budurwarsa Miliyan 10 da sunan ta sama musu inda zasu zauna bayan sun yi aure. Saidai ko da ya zo Najeriya sai ya tarar ta karkatar da Kudin sannan kuma ta fara soyayya da Wani.

 

Budurwar me suna Mary ta kuma kulle duk wani layin wayar da Emmanuel zai same ta canja gurin zama.

 

PMExpress ta ruwaito cewa, Emmanuel ya kai kara wajan ‘yansanda inda kuma suka gano Mary a inda take boye, an nemi ta mayar masa da kudinsa amma tace ta kashesu gaba daya.

A karshe dai an gabatar da ita a Kotu inda amma ta ki amsa laifinta. Saidai dansanda me gabatar da kara, Bernard ya nemi kotu ta bada lokaci dan ya kawo hujjojinsa. Kuma Kotu ta amince inda ta saka ranar 19 ga watan Afrilu a matsayin ranar ci gaba da shari’ar. Saidai an bada binta akan Naira Miliyan 3.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *