fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

Buhari ya amince da Abubakar Nuhu Fikpo a matsayin Mukaddashin Shugaba na hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Malam Abubakar Nuhu Fikpo a matsayin mukaddashin Darakta-Janar na hukumar samar da ayyukan yi ta kasa (NDE).
Wannan ya na kunshe ne a cikin wata wasika zuwa ga Karamin Ministan, Kwadago da Aiki, Festus Keyamo (SAN), mai kwanan wata Litinin 18, 2021.
Wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce nadin zai ci gaba har zuwa lokacin da za a nada wani Babban Darakta-Janar.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya isar da sanarwa ga Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Mista Festus Keyamo, SAN, kan amincewarsa da nadin Malam Abubakar Nuhu Fikpo a matsayin Mukaddashin Darakta-Janar na hukumar samar da Ayyuka na Kasa.
Sanarwar ta ce “A watan da ya gabata, shugaban kasar ya sauke tsohon DG na hukumar daga nadin nasa, kuma ya umarci Ministan da ya zabi wani Mukaddashin DG mai kula da Hukumar har zuwa lokacin da za a nada wani DG”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *