
Bidiyo: Wani matashi ya bada labarin yadda yayiwa surukarsa ciki wacce daga baya ta haifi da namiji
Wani matashi dan Nageriya ya ba da cikakken bayani game da abin da ya faru da surukarsa a wani shirin kira da aka yi a Nigeria Info, ya ce an gabatar da shi ga surukarsa ne yayin da har yanzu yake tare da matarsa.
A cewarsa, sun yi lalata bayan sun hadu a wani “wurin shakatawa” tare da wasu abokai.
Mutumin wanda ya bayyana cewa ya bugu sosai da giya a lokacin, ya ce ya kadu bayan da ya samu labarin cewa surukarsa ta ci gaba da daukar jaririn wanda ta manne wa mijinta a matsayin dansa.
Mutumin ya kuma bayyana cewa lokacin da ya tambayi surukarsa dalilin da ya sa ta haihu, sai ta ce ta dauki matakin ne saboda mijinta yana mata gori a koda yaushe saboda diya mata kawai ta haifa masa.
Mutumin ya kuma bayyana yadda yake bakin cikin sanin cewa yanzu dan nasa ne kuma surukinsa ne....