fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Crime

Zan fito takarar shugaban kasa a shekarar 2023, kuma idan ban cika Alkawarin da na yi ba a Bankareni a harbe>>Doyin Okupe

Zan fito takarar shugaban kasa a shekarar 2023, kuma idan ban cika Alkawarin da na yi ba a Bankareni a harbe>>Doyin Okupe

Crime, Siyasa
Tsohon kakakin shugaban kasa, a zamanin Mulkin Goodluck Jonathan,  Doyin Okupe ya bayyana cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023.   Yace yana da tsari me kyau na yanda zai inganta tattalin arziki da kuma magance matsalar tsaron.   Saidai yace idan bai cika alkawarin da ya dauka ba, to a shirye yake a bankareshi a harbe. Ya bayyana hakane a hirar da yayi da Vanguard. “No president has ever given a detailed explanation of how they intend to tackle insecurity, improve the economy is this country. They always don’t give a blueprint. “I have a masterplan to eradicate insecurity, particularly the activities of banditry. If the situation continues the same way, I am going to run for presidency. "I am ready to face firing squad...
Kiwan Lafiya: Gwamantin Kano ta rufe wani Dakin gwaje-gwaje da bashi da rijista

Kiwan Lafiya: Gwamantin Kano ta rufe wani Dakin gwaje-gwaje da bashi da rijista

Crime
Gwamnatin jihar Kano ta kulle wani katafaren dakin binciken likitanci a karamar hukumar Minjibir da ke aiki ba tare da rajista ba. Babban Sakataran Hukumar Kula da Lafiya na Cibiyoyin (PHIMA), Dokta Usman Tijjani Aliyu shine ya sanar da haka a ranar Laraba a wata hira da yayi da manema labarai a jihar Kano. Sakataren zartarwar ya ce, '' samamen ya biyo bayan korafe-korafen da aka samu daga mutanen da abin ya shafa dake karamar hukumar kan haramtattun ayyuka da ake yi a dakin gwaje-gwaje wadanda hakan ya sabawa dokokin hukumar. Dan haka a cewarsa, za a hukunta duk wanda aka kama da laifin hakan.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ta yi Nasarar cafke wasu masu garkuwa da Mutane

Rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ta yi Nasarar cafke wasu masu garkuwa da Mutane

Crime
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba tayi Nasarar kama mutane tara da ake zargi da yin garkuwa da wani Dan Majalisar Dokokin jihar Mohammed Bashir Bape, wanda aka sace shi tun a watan Disamban shekarar 2020. An kama wadanda ake zargin ne a maboyarsu dake a Jihohin Taraba da Filato bayan wani bincike da rundunar ‘yan sanda ta gudanar domin cafke masu laifin. Wadanda ake zargin sun hada da, Yusuf Abubakar, mai shekaru 31 dan asalin karamar hukumar Jalingo dake a jihar Taraba, sai Muntari Umar, mai shekaru 27, dan asalin karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa, Ahmadu Dahiru, mai shekaru 28, dan asalin karamar hukumar Lau, jihar Taraba, Ali Alhaji Wurungo mai Shekaru 25, dan asalin karamar hukumar Lau ta jihar Taraba, Buhari Nuhu, dan shekaru 25, dan asalin karamar hukumar Jalingo, Moh...
NDLEA ta cafke wasu Dillalan tabar wiwi a jihar Dalta

NDLEA ta cafke wasu Dillalan tabar wiwi a jihar Dalta

Crime
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wasu mutane uku bisa laifin safarar buhu 690 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 414. Rundunar tayi Nasarar kama biyu daga cikin wadanda ake zargin, da suka hada da Anthony Osoria da Onyeka Okoronkwo. Kwamandan hukumar na jihar, Obiefule Dennis, shine shaida hakan ga Manema labarai.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta gano wani sito ajiye da tabar wiwi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta gano wani sito ajiye da tabar wiwi

Crime
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar gano wani sito makare da tabar wiwi a garin, Fatakwal dake jihar Ribas. Hukumar ta NDLEA, ta shaida hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta bayyana cewa ta yi nasarar kame kayan ne sakamakon wasu bayanan sirri da hukumar ta samu. Hukumar ta kara da cewa jami’anta sun kutsa kai cikin rumbun ajiyar kayan mayan ne da safiyar ranar Asabar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2021 inda suka gano wasu buhu 23 na buhunan tabar wiwi masu nauyin kilogram 621 da hodar iblis mai nauyin 0.029kg.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Delta sun kama wani mutum bisa laifin yin lalata da yarinya’ yar shekara bakwai

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Delta sun kama wani mutum bisa laifin yin lalata da yarinya’ yar shekara bakwai

Crime
Jami'an rundunar 'yan sandar jihar Delta sun kama wani mutum mai shekaru 73 da haihuwa mai suna Madumeye bisa zargin lalata da yarinya' yar shekara bakwai. Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya shiga hannu ne a ranar 19 ga watan Fabrairu, bayan da ake zarginsa da lalata da wata yarinya. An bayyana cewa wanda ake zargin ya sanya yatsun sa cikin Matucinta wanda hakan ya haifar da canji daga ya rinyar da har mahaifiyarta ta lura da sauyin 'yar tata. Bayan Mahaifiyar ta gano hakan ne yasa ta tambayar 'yar tata inda ta shaida mata wanda ya aikata mata lamari.  
Hukumar KAROTA ta cafke wasu jabun Magun-guna

Hukumar KAROTA ta cafke wasu jabun Magun-guna

Crime
Hukumar KAROTA dake jihar Kano ta cafke wasu kayayyaki da hukumar ke zargin magun-guna ne da basu da rijista. Kakakin hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na'isa shine ya sanar da hakan ga manema labarai a jihar Kano. A cewara anyi Nasarar cafke motar dakun kayana ne da misalin karfe 3 na dare a kan titin Igbo road dake sabon gari a karamar hukumar Fagge. Da yake magana kan wadanda su ka daukko dakon kayan ya ce tuni sun ka tsere.
‘Yan bindiga sun kashe‘ yan sanda 2 a Delta

‘Yan bindiga sun kashe‘ yan sanda 2 a Delta

Crime
Rundunar ‘yan sanda a jihar Delta ta tabbatar da kisan wasu jami’anta biyu da‘ yan bindiga suka yi, a kan hanyar Ugbolu-Illah dake a karamar hukumar Oshimili  da ke jihar. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Mohammed Ali, ya tabbatar da kisan ga manema labarai ranar Talata a Asaba. Ya ce duk da haka 'yan sanda sun kashe biyu daga cikin' yan bindigar, amma anyi rashin sa'a harbe-harben bindiga daga 'yan sanda yayi sanadin mutuwar wata tsohuwa a yayin artabu da maharan. Rundunar ta bayyana cewa tana kokarin tattaunawa da Dangin tsohowar domin ganin anyi wani Abu. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Asabar a kusa da wani sanannen wurin shakatawa, dake Lake Town Hotel.  
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu mutum 7 bisa laifin satar mota

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu mutum 7 bisa laifin satar mota

Crime
Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta dakume wasu matasa data kama da laifin satar mota kwanaki kadan bayan sakin su daga gidan gyara kan makamancin laifin. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Orlando Ikeokwu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Owerri. Ikeokwu, ya ce an samu nasarar cafke su ne bayan da rundunar ta samu rahoto daga wasu mazauna dake yankin Aba a jihar.  An dai zargi Matasan ne da satar mota kirar LEXUS 350 SUV. Sai dai lokacin da aka tuhumesu da laifin sun Amsa laifinsu.  
Gwamnatin Neja ta ceto matafiya 10 daga cikin 21 da ‘yan bindiga suka sace

Gwamnatin Neja ta ceto matafiya 10 daga cikin 21 da ‘yan bindiga suka sace

Crime
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da ceto akalla mutane 10 daga cikin mutane 21 da 'yan bindiga suka sace a jihar. Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Mohammad Dani Idris, shine ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Talata, a Babban Asibitin jihar dake Minna a a yayin da likitoci ke duba lafiyar wadanda aka ceto. Hakanan kwamishinan ya musanta rade-radin biyan fansa wajan ceto wadanda a kai garkuwa dasu inda ya shaida cewa gwamnati tabi wasu dabaru ne wajan ceto mutanan.