fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Uncategorized

An bayar da Shawarar a rika aure tsakanin Kirista da Musulmai dan gujewa raba Najeriya

An bayar da Shawarar a rika aure tsakanin Kirista da Musulmai dan gujewa raba Najeriya

Tsaro, Uncategorized
Ministan yada labarai da al'adu, Lai Muhammad ya bayyana cewa zai gabatar da shawara da masana suka bayar a Kaduna dan kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya ga majalisar zartaswa.   Yace daya daga cikin shawarwarin da aka bayar dan gujewa raba Najeriya shine a rika aure tsakanin Jinsi da kuma addinai daban-daban.   Ya bayyana cewa kamata yayi Yarbawa su rika auren Inyamurai, Itsekiri da  Hausawa ma su yi aure, yace idan aka yi irin wannan aure da wuya a raba Najeriya.   “Christians are encouraged to marry Muslims, Itsekiri should marry Hausa, Yoruba should marry Igbo, when you have that kind of intermarriage, it becomes more difficult to break the country.” NAN    
Bidiyo: Kalli yanda Budurwa ta kunyata Saurayinta a bainar jama’a bayan kamashi da kanwarta, ta kwace waya, takalmi da sauran kayan data sai masa

Bidiyo: Kalli yanda Budurwa ta kunyata Saurayinta a bainar jama’a bayan kamashi da kanwarta, ta kwace waya, takalmi da sauran kayan data sai masa

Uncategorized
Wata budurwa ta fallawa Saurayinta Mari ta kuma kwace takalmi da bel da wayar hannu data sai masa.   Ta mai wannan rashin mutunci ne bayan kamashi da kanwarta suna soyayya a bainar jama'a.   Bidiyon lamarin ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta.   https://twitter.com/MustaphaOlatu19/status/1384767150339108866?s=19  
Ƙungiyoyin Ingila sun janye daga European Super League

Ƙungiyoyin Ingila sun janye daga European Super League

Uncategorized, Wasanni
Kungiyoyi shida da ke buga wasan Firimiyar Ingila da ke cikin sabuwar gasar da aka ƙirkira ta European Super League sun sanar da janyewa daga gasar. Arsenal da Liverpool da Manchester United da Tottenham su bi sahun Chelsea da Man City, da suka sanar da janyewarsu tun da fari. Barazanar kafa gasar ta manyan ƙungiyoyin Turai ta ja hankali tare da martani daga hukumomin ƙwallon ƙafa da shugabannin Turai. Gasar da aka ƙirƙira a ranar Lahadi,jagoran gasar ya ce zai duba yadda zai sake sabunta shirin. Hukumar kwallon kafa ta Uefa ta yi maraba da matsayin kungiyoyin. Manyan kulob mafi arziki 12 a Ingila da Sifaniya da Italiya da suka ɓalle domin kafa wannan league din sun sha Allah wadai daga magoya bayansu da gwamnatoci. Shugaban Uefa ya yi alƙawalin haɗa kan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ta...
An shiga rudani yayin da ake rade-radin mutuwar dan Shugaban kasar Chadi

An shiga rudani yayin da ake rade-radin mutuwar dan Shugaban kasar Chadi

Uncategorized
An shiga Rudani a kasar Chadi yayin da ake rade-radin cewa, an kashe dan Marigayi Shugaban kasar Chadi watau Mahamat Derby.   An fara rade-radin ne a shafukan sada zumunta inda kuma daga baya kafafen yada labaran kasar suka dauka.   BBC ta ruwaito cewa an ji harbe-harbe a cikin fadar Shugaban kasar. Ana tsammanin lamarin ya farune Saboda raahin jituwa da ta kaure ka wamda zai gaji Idris Derby.   Saidai wata kafar yada labarai ta kasar Tchadinfos ta ruwaito wasu Majiyoyi na musanta lamarin. Amma wata majiya, daga kafar Toubou Media ta bayyana cewa dan Shugaban kasar ya ji raunine a tashin jituwar. Marigayin ya auri mata da yawa inda yake da 'ya'ya da ba'a kai ga tantance yawansu ba.
Majalisa na kokarin ganin an rage farashin Siminti

Majalisa na kokarin ganin an rage farashin Siminti

Uncategorized
Majalisar tarayya ta fara wani yunkuri da zai kai ga rage farashin Siminti a Najeriya. Majalisar ta jawo hankalin Gwamnatin tarata ta sassauta dokar kafa masana'antu dan a samu masu saka jari a bangaren.   Hakan na zuwane bayan da Sanata Ashiru Oyelola Yisa ya gabatar da kudiron a gaban majalisar.   Majalisa ta nemi da gwamnati ta sassauta Haraji a bangaren ta yanda za'a samu masu saka hannun jari na gida su shiga harkar.
Akwai makarantu 62,000 da za’a iya kaiwa Hari a Najeriya>>Minista Kudi

Akwai makarantu 62,000 da za’a iya kaiwa Hari a Najeriya>>Minista Kudi

Siyasa, Uncategorized
Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa, akwai makarantu 62,000 da suke cikin hadarin kai musu hari a Najeriya.   Ta bayyana hakane ranar Talata a wajan wai taro da aka tattauna yanda za'a ciyar da makarantun Najeriya gaba a Abuja.   Zainab ta bayyan cewa zasu samar da yanayin karatu me kyau ga daliban kuma zasu hada hannun da bangaren masu zaman kansu dan dan cimma wannan manufa. “62,000 schools are physically porous and this is a very large number. This is not to say that building a fence actually stops abductions. “We must also educate children, teachers and communities and put alarm systems in place. Like the head of civil defence says, educate the communities to know what to expect and identify telltale signs of abduction. “We will come ...
Pantami Mutum ne me kima da tsare doka, wasu ne da basu son zaman lafiya ke Kiraye-kirayen saukeshi>>Wata Kungiyar Fafutuka a Legas

Pantami Mutum ne me kima da tsare doka, wasu ne da basu son zaman lafiya ke Kiraye-kirayen saukeshi>>Wata Kungiyar Fafutuka a Legas

Uncategorized
Wata kungiyar dake fafutuka kan rajin kare hakkin Bil'adama dake Legas ta bayyana goyon bayanta ga Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.   Kungiyar tace Pantami Mutum ne me bin doka da kuma Basira sannan yana daga cikin manyan jami'a gwamnatin Buhari.   Kungiyar me suna Coalition of civil society for good governance wadda hadakar wasu kungiyoyin fafutuka ce ta bakin Shugabanta, Declan Ihekaire ta bayyana cewa, kiraye-kirayen sauke Pantami, wasu manyan mutanene suka dauki nauyinsa wanda basu son zaman lafiya a Najeriya.   Kungiyar tace fitowar da Pantami yayi ya amsa cewa yayi waccan magana sannan yayi bayanin dalili, abun yabo ne wanda ba kowane zai iya ba, tace hakan ya nuna cewa Ministan nada gaskiya da kuma Kishin kasa. ...
Na kadu da Mutuwar Shugaban Chadi, Munyi babban Rashi>>Shugaba Buhari

Na kadu da Mutuwar Shugaban Chadi, Munyi babban Rashi>>Shugaba Buhari

Uncategorized
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi shugaban kasar Chadi Idris Deby da ‘jajirtaccen shugaba’, wanda mutuwarsa za ta bar gagarumin gibi a yakin da kasashen duniya ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda. Yayin da yake bayyana kaɗuwa da kashe Idris Debby da ‘yan tawaye suka yi, Shugaba Buhari ya ce mutuwar shugaban mai shekara 68 za ta bar babban giɓi a ƙoƙarin hadin gwiwa da ake yi na murƙushe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP. Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta Ambato Shugaba Buhari na cewa ‘Ina cikin alhini da kaɗuwa kan mutuwar Shugaba Idris Deby a fagen daga a ƙoƙarin da yake yi na kare kasarsa.’’ Shugaban Najeriyar ya jinjina wa marigayi Idris Deby a yaƙin da yake yi da kungiyar Boko Haram, ya kuma kira shi da ‘’babban abokin Najeriya. "Sannan ya sanya...
Tunda aka kafa Najeriya ba’a taba samun gwamnati kamar ta Buhari ba>>APC

Tunda aka kafa Najeriya ba’a taba samun gwamnati kamar ta Buhari ba>>APC

Uncategorized
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, tunda aka kafa Najeriya, ba'a taba samun Shugaban kasa kamar Muhammadu Buhari ba.   Sakataren Kwamitin Riko na jam'iyyar APC, John Edehe ne ya bayyana haka a wajan ganawa da manema labarai.   Yace amma masu sukar gwamnatib sun rufe ido basa fadar gaskiya. Yace babu gwamnatin data taba Talakawa kai tsaye kamar ta Shugaba Buhari.
Kasar Ingila nawa Najeriya zagon kasa kan yaki da ta’addanci>>Gwamnatin Tarayya

Kasar Ingila nawa Najeriya zagon kasa kan yaki da ta’addanci>>Gwamnatin Tarayya

Tsaro, Uncategorized
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, kasar Ingila na mata zagon kasa wajan yaki da ta'addanci.   Ministan Yada Labarai da Al'adu Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka a wajan wani taron ganawa da manema labarai da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya shirya.   Lai Muhammad yace muddin maganar baiwa 'yan IPOB da MASSOB mafaka a kasar Ingila ta tabbata to lallai haka raini ne ga Najeriya da kuma yiwa kasar zagob kasa a yako da ta'addanci.   “Let me say straightaway that this issue is within the purview of the Honourable Minister of Foreign Affairs and I am sure he will handle it appropriately. “But as the spokesman for the Federal Government of Nigeria, I will say that if indeed the report that the UK will grant asylum to supposedly persecuted IPOB a...