fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Coronavirus ta kashe Amurkawa sama da dubu 3 a kwana daya

Sama da mutane miliyan 2 da dubu 675 suka kamu da kwayar cutar a kasashen duniya 193, inda fiye da dubu 700 suka warke.

Kasar Amurka kadai, cutar ta kashe kusan mutane dubu 50, da suka hada da dubu 3 da 176 da ta kashe cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Amruka ce ke sahun gaba wajen samun asarar rayuka, italiya ce ke matsayi na biyu da asarar mutane dubu 25 da 549 , sai kuma dubu 23 da 157 da suka mutu a Spain, yayin da a Fransa, adadin mamatan ya kai dubu 21 da 856, sai kasar Birtaniya da ta yi asarar mutane dubu 18 da 738 a sanadiyar annobar ta coronavirus.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *