Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kori Hadimansa, Salihu Tanko Yakasai saboda caccakar shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan matsalar tsaro.
Kwamishinan yada labaran Jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda yace dakatarwar zata fara aiki ne nan take.
Yace Hadimin gwamnan ya kasa banbance ra’ayinsa da kuma aikinsa da yake yi.