fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Da Duminsa:An ci gaba da kai kayan Abinci kudu

Mutanen jihar Kwara da sauran jihohin Yarbawa sun dara da yammacin yau bayan da tireloli dauke da abinci daga Arewa suka ci gaba da jigila.

 

A makon da ya gabata ne dai aka samu wasu fusatattu suka hana motocin dake dauke da abinci daga Arewa shiga kasashen Yarbawa.

 

Dalilin haka yasa aka tara tsaikon motoci da yawa inda kuma Rahotanni suka bayyana cewa wasu kayan Abincin ma sun fara lalacewa. Wani dan kasuwa, Alhaji Adebara ya bayyanawa Punchng cewa sojoji ne suka je wajan suka tursasa ci gaba da jigilar kayan.

 

Sannan sun bayyana cewa duk wanda ya sake ya tare hanyar zasu daukeshi a matsayin dan taadda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *