Dayawan Sojojin Nijeriya sun mutu a ranar Litinin lokacin da wani dan ta’adda na kungiyar Boko Haram ya kutsa kai cikin wata mota makare da bama-bamai a yayin wani artabu a jihar Yobe, kamar yadda wata majiyar soji ta shaida wa SaharaReporters.
Dan kunar bakin waken, wanda ake kyautata zaton dan kungiyar ISWAP ne, ya auna ayarin sojojin ne a Goniri, wani yankin kan iyaka tsakanin jihohin Yobe da Borno.
SaharaReporters ta tattaro cewa maharan sun kuma yi artabu da sojojin Najeriya.
“Akwai wani harin SVBIED ( Motor kai Hare-Haren Kunar Bakin Wake) a Goniri jiya, don haka sojoji da yawa sun mutu kuma sun ji rauni. A halin yanzu ba a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba, ”in ji wata majiyar soja.
A ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar ta kashe mutane biyar da ke gudun hijira a cikin jihar ta Borno.