fbpx
Monday, June 14
Shadow

Dan majalisa, Ahmad Jaha daga Borno ya bada hakuri kan maganar da yayi ta cewa shigar banza ce da mata ke yi ke sawa a musu fyade

Dan majalisar wakilai daga jihar Borno, Ahmad Jaha ya bayar da hakuri kan maganar da yayi ta cewa shigar banza da mata ke yi ce ta sa masu fyade ke jan hankali zuwa garesu.

 

Dan majalisar a ganawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya bayyana cewa maganar da yayi a lokacin zaman majusar ta cewa shigar banzar matace ke jawo fyade bata dace ba.

Yace ko wane irin kaya mace ta saka ba dali bane na a mata fyade ba. Yace a lokacin da yake magana ya bada shawarar a yankewa masu fyade hukuncin kisa to ba wai yana kokarin dorawa mata laifin fyaden da ake musu bane akan shigar da suke.

 

Yace yana bada hakuri ga duk wani dan Najeriya, musamman mata da maganar tasa ta batawa rai dama sauran abokan aikinshi yace duk a yi hakuri a yafe masa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *