fbpx
Saturday, March 6
Shadow

Daya daga cikin shuwagabannin kananan hukumomin da aka zaba a Kano ya mutu sa’o’i 48 bayan zaben shi

Kimanin awanni 48 bayan bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kano da Shugaban Hukumar Zabe ta Kano (KANSIEC) ta sanar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka sabon zababben shugaban karamar hukumar Bebeji, an tabbatar da mutuwar Hon Ali Nnamandi.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban kwamitin yada labarai na APC a karamar hukumar Bebeji, Honarabul Ibrahim Adamu Tiga, wanda aka gabatar wa manema labarai a ranar Talata a Kano, zababben shugaban ya mutu da sanyin safiyar Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ya bayyana a cikin sanarwar cewa marigayi Hon. Nnamandi ya tuka kansa zuwa wani Asibiti mafi kusa a karamar hukumar, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa bayan gajeriyar rashin lafiyar da ake zargin ta cutar hawan jini.
Tiga ya tabbatar da za a binne Nnamabdi a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.
Idan ba a manta ba, an zabi marigayi Hon, Nnamabdi a matsayin shugaban karamar hukumar Bebeji a zaben karamar hukumar da aka kammala ranar Asabar da ta gabata.
Ya lashe zaben ne a karkashin jam’iyyar APC kamar yadda shugaban KANSIEC, Farfesa Garba Ibrshim Sheka ya sanar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *