fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Dillalan Shanu Za Su Fara Yajin Aiki a Duk Fadin Najeriya a Yau

Dillalan shanu da na Abinci a karkashin hadaddiyar kungiyar hadahadar abinci da dillalan shanu ta Najeriya (AUFCDN), a yau za su fara yajin aiki a duk fadin kasar nan bayan cikar wa’adin kwanaki bakwai da aka ba gwamnatin tarayya domin ta biya masu bukatunsu.

A ranar Lahadi ne Kungiyar AUFCDN wadda ta hade da Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC ta ce, tana son gwamnati ta bai wa mambobinta kariya tare da biyan ta diyyar Naira biliyan 475 saboda kisan da aka yi wa ‘ya’yanta da kuma asarar da ta tafka a lokacin zanga-zangar EndSARS da kuma rikicin kasuwar Shasa da ke garin Ibadan.

 

Kazalika kungiyar ta bukaci gwamnati da ta bada umarnin janye shingayen binciken ababan hawa da aka kafa a manyan hanyoyin kasar saboda matsalolin da mambobinta ke fuskanta a yayin gudanar ada harkokinsu na jigilar abinci da shanu.
Daya daga cikin jiga-jigan kungiyar ta AUFCDN, Hajiya Hauwa Kabir Usman, ta bayyana cewa, an tanadi jami’an kungiyar da za su tabbatar da cewa, ba a yi jigilar shanu da abinci daga arewaci zuwa kudancin Najeriya ba a yayin wannan yajin aikin.
Ta kara cewa “Duk motar da zata fita sai an duba ta. Idan kun ɗauki wani abinci ko shanu, ba za ku iya fitar da shi ba, sai dai in kun komo da shi ko a lalata shi. Babu wani daga cikin jami’an tsaro da ya isa ya kuskura ya kalubalanci mambobin kwamitinmu domin idan suka yi hakan, za mu yi fada da shi ta hanyar da ta dace. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *