fbpx
Friday, March 5
Shadow

Duk Labarai

Da Maryam Sanda tayi irin wannan tunanin da bata kashe mijintaba:Karanta abinda wata mata tawa mijinta bayan ta ga sakon budurwashi

Uncategorized
Wasu mutanen Allah yayi musu hikimar iya warware matsala ta hanya me sauki ba tare da kowa ma yasan me ya faruba, labarin wata matace a jihar Adamawa da ta kama mijinta yana hirar soyayya da wata budurwa a waje, taga sakonnin soyayyar da mijin nata da budurwarshi suka aikawa junanshu ta dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook. Ta zauna abin ya isheta, tana ta takaici da tunanin yanda zata bullowa wannan lamari, can sai wata dabara ta fadomata. Ta lallaba ta dauki wayar mijinnata ta kwashe duk sakonnin da mijin nata da budurwarshi suka aikawa junansu na soyayya. Taje ta bude sabon dandalin sada zumunta a facebook da sunan namiji, ta aikawa mijinnata  da gayyatar abota, ba tare da yasan cewa itaceba kuma akayi sa'a ya amshi gayyatar abotan. Bayan sun gaisa, sai ta g...

Gwamnan jihar Nasarawa ya bayar da motarshi akai wasu yara, ‘yan makaranta gida, bayan da ya hadu dasu wani dan acaba ya kwasosu su biyar akan mashin

Uncategorized
Gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko Almakura kenan a wannan hoton, yana tafiya da tawagarshi yaga wannan dan acabar yayi mugun lodi da yara, 'yan makaranta, ya tsaya ya gargadi dan acabar da ya daina irin wannan gangancin lodin da yaran mutane. Anan kuma ya bayar da daya daga cikin motocinshi aka kai yaran har gidansu. Mutane da dama sun yabamai akan wannan abin alheri da yayi. Saidai wasu sunce kamata yayi gwamnan ya bayar da motar da za'a rika dakko yaran makarantar, tunda gobe in sun taso, wa zaikaisu gida?.

Beraye, kyankyasai da kuma kwari sun mamaye fadar shugaban kasar Amurka

Uncategorized
Ma'aikata a fadar shugaban kasar Amurka ta White House, sun koka da mamayar da beraye, kyankyasai da kuma kwari sukawa ofisoshinsu, wannan ya bayyanane a cikin wata takardar gyare-gyare da aka yiwa fadar. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kafar watsa labarai ta NBC ce ta bayyana cewa ta samu takardun gyaran da akawa fadar shekaru biyu da suka gabata, inda aka bukaci bangarorin ma'aikata daban-daban su mika irin gyare-gyren da dakuna da ofisoshinsu ke bukata. A cikin takardun da aka mika na bukatar gyaran akwai wanda ofishin shugaban ma'aikata na fadar ya mika inda yayi korafin cewa ofishin nashi kwari sun addabeshi saboda haka yana bukatar gyara. A shekarun bayane rahotanni suka bayyana cewa beraye sun hana shugaban kasa Muhammadu Buhari shiga Ofishinshi ba...