fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

EFCC ta kama mutum 20 da take zargi da damfara A yanar gizo

Mutum 20, da ake zargi da zamba ta yanar gizo a ranar Juma’a sun shiga hannun jami’an ofishin shiyyar na Fatakwal na Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’anci, EFCC.

Hukumar a cikin wani sako da ta wallafa a ranar Litinin ta ce an kama wadanda ake zargin ne a Owerri dake a Jihar Imo.

Wadandaa aka kama sun hada da  ”Onyebuchi Victor; Isreal Victor; Emeka Clinton; Stanley Uche; Onyemachi Stanley; Ikechukwu Agbalieze; Franklin Ugoegbu; Nze Collins; Nwokoro Santus da Agocha Johnson da sauran su.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da: wayoyin hannu guda arba’in (40), kwamfutocin tafi-da-gidanka goma sha bakwai (17) da motoci 6 tare da sauran kayyayaki.

Hukumar ta ce zata gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan ta kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *