A yan kwanakin nan Hauhawar farashin man gyada a Kano ya sabba karuwar farashin Awara da sauran kayan da ake sarrafawa da man gyada.
A wani bincike da Hutudole ta yi a birnin Kano ya gano cewa Awara ta yi tashin gwauron zabo, sakamakon karuwar farashin man gyada a fadin jihar.
Binciken ya gano cewar a watanni 2 zuwa 3 da suka wuce baya ana sayar da kwalbar man kuli akan N450, da a yanzu kuma ake sayarda kowacce kwalba akan N600zuwa N650.
Haka kuma a yanzu ana sayar da karamin galan akan N5000, sabanin yadda ake sayar dashi a baya da bai gaza N300 ba.
Kafin karin kudin man kuli dai a Kano ana sayar da Awara akan naira 10, sai dai a yanzu saboda karin kudin mangyada sai dai a sayar guda Uku 50, wadanda ba su kara farashin ba kuma to sun rage hannu.
Da na tambaya me yasa kudin mangyadan ya karu sai aka cemin wai yanzu ba a noma gyada, a kasar nan yawanci ana kawo ta ne daga Senegal.
Jama’a da dama dai a Kano na kokawa akan irin wannan tsadar ta mangyada da sauran kayayyaki wanda hakan na zuwa ne a daidai lokacin da talaka ke cikin mawuyacin hali.