fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

Gobara ta kona shaguna a kasuwar ‘Yan Katato, Sabon Gari, Zariya

Gobara ta kone kayyaki na miliyoyin Naira a sanannen kasuwar ‘Yan Katato, karamar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna.
Shugaban, kungiyar Kafinta na Sabon Gari, kasuwar Yan Katato, Sabon Gari, Zariya, Suleiman Yusuf-na-Hari, ya bayyana cewa gobarar da ta faru a kasuwar ranar Juma’a, ta lalata shaguna da kayayyakin daki na miliyoyin Naira.
Ya bayyana cewa lamarin gobarar ya faru ne da misalin karfe 4 na asuba kuma kusan kashi 50 na shagunan abin ya shafa.
Shugaban ya koka kan yadda lamarin gobarar ya kasance mafi munin da ba a taba yin irinsa ba a tarihin kasuwar.
Ya lura cewa akwai kusan shaguna 600 da ke aiki a kasuwar, kuma sama da rabin shagunan ne lamarin ya shafa.
Suleiman Yusuf-na-Hari ya yi amannar cewa lamarin gobarar na da nasaba da tartsatsin wuta daga ɗayan injunan da ke kasuwar bayan ya fitar da wasu abubuwa masu zafi.
Shugaban ya lura cewa jami’an tsaron da ke gadin kasuwar ba za su iya hana yaduwar gobarar ba, yana mai bayanin cewa sai da hukumar kashe gobara ta jihar ta dauki matakin shawo kan gobarar da misalin karfe 10 na safe, bayan awanni shida.
Ya jajantawa wadanda abin ya shafi shagunan da gobarar ta lalata sannan ya umurce su da su dauki lamarin da aminci.
Shugaban kungiyar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da karamar hukumar da su hanzarta zuwa ga wadanda abin ya shafa na tashin gobarar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *