Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana dalilin da yasa ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yammacin jiya, Talata.
Yace ya yiwa shugaban kasar Jawabi ne kan halin da ake ciki a kasar Gambia.
Shugaba Jonathan ya bayyana cewa wannan mataki ne na farko na sasanci da shiga tsakani kuma nan da watan Janairu zai sake komawa kasar.
Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow na fuskantar matsin lamba daga ‘yan Adawa akan ya mutunta alkawarin da yayi na cewa Zango 1 kawai zai yi na mulkinsa.