Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, a ranar Talata ya yi tir da kalaman da Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, yayi akan kiran Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed dan ta’adda.
Da yake mai da martani kan maganganun da Ortom ya yi, Femi ya bayyana cewa Bala Mohammed mutum ne wanda baya nuna wariyar a kan addini ko tsakanin kabilu, kiran shi dan ta’adda babban kuskure ne.
Femi wanda ya bayyana hakan a cikin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ya san gwamnonin da ke da hannu a ta’addanci da ake yi a Najeriya kuma idan Ortom na son ya sanar da shi, zai gaya masa.