fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Gwamna Ganduje ya bada tallafin N3m ga mutumin da ya rasa iyalansa 7 a gobarar kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da gudummawar Naira miliyan 3 ga Malam Abdulrahaman Ibrahim Wailari domin rage masa radadi da asarar da ya yi a wani bala’in gobara da ya mamaye gidansa kwanan nan.

Wailari, mazaunin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, ya rasa iyalansa bakwai a sanadiyar wannan gobara.

An sanar da bayar da gudummawar ne yayin bikin kaddamar da rabon kayayyakin tallafin ga mutane 1500 a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *